1 Corinthians 1

1Bulus, kirayayye daga Almsihu Yesu don zama manzo ta wurin nufin Allah, da dan’uwanmu Sastanisu, 2zuwa ga Ikilisiyar Allah da ke korinti, zuwa ga wadanda aka kebe su cikin Almasihu Yesu, wadanda aka kira domin su zama al’umma maitsarki. Muna kuma rubuta wa dukan masu kira bisa sunan Ubangijinmu Yesu Almasihu a ko’ina, wato Ubangijinsu da Ubangijinmu kuma. 3Bari alheri da salama su zo gare ku daga Allah Ubanmu da Ubangiji Yesu Almasihu.

4Kodayaushe ina gode wa Allahna domin ku, saboda alherin Allah da Almasihu Yesu ya yi maku. 5Ya ba ku arziki ta kowace hanya, cikin dukkan magana da dukkan ilimi. 6Kamar yadda shaida game da Almasihu ta tabbata gaskiya a tsakaninku.

7Saboda haka baku rasa wata baiwa ta ruhaniya ba yayinda kuke marmarin jiran bayyanuwar Ubangijinmu Yesu Almasihu. 8Zai kuma karfafa ku zuwa karshe, saboda ku zama marasa aibi a ranar Ubangijinmu Yesu Almasihu. 9Allah mai aminci ne shi wanda ya kira ku zuwa zumunta ta Dansa, Yesu Almasihu Ubangijimu.

10Ina rokon ku, yan’uwa, cikin sunan Ubangijinmu Yesu Almasihu, ku yarda da juna, kada tsattsaguwa ta kasance tsakanin ku. Ina rokon ku ku zama da zuciya daya da kuma nufi daya. 11Gama mutanen gidan Kulowi sun kawo kara cewa akwai tsattsaguwa a cikin ku.

12Ina nufin: kowannen ku na cewa, “Ina bayan Bulus,” ko “Ina bayan Afollos,” ko “Ina bayan Kefas,” ko “Ina bayan Almasihu.” 13Almasihu a rarrabe yake? An gicciye Bulus domin ku? Ko an yi maku baftisma a cikin sunan Bulus?

14Na godewa Allah domin ban yi wa wanin ku baftisma ba, sai dai Kirisfus da Gayus. 15Na yi wannan saboda kada wani ya ce an yi maku baftisma a cikin sunana. 16(Na kuma yi wa iyalin gidan Sitifanas baftisma. Banda haka, ban sani ko na yi wa wani baftisma ba.)

17Gama Almasihu bai aiko ni domin yin baftisma ba, amma domin yin wa’azin bishara. Bai aiko ni domin in yi wa’azi da kalmomin hikimar mutum ba, saboda kada giciyen Almasihu ya rasa ikonsa.

18Gama wa’azin gicciye wauta ne ga wadanda su ke mutuwa. Amma cikin wadanda Allah ke ceto, ikon Allah ne. 19Gama a rubuce yake, “Zan watsar da hikimar masu hikima. Zan dode fahimtar masu basira.”

20Ina mai hikima? Ina masani? Ina mai muhawara na duniyan nan? Allah bai juya hikimar duniya zuwa wauta ba? 21Tunda duniya cikin hikimarta bata san Allah ba, ya gamshi Allah ta wurin wautar wa’azi ya ceci masu bada gaskiya.

22Gama Yahudawa suna bidar al’ajibai, Helinawa kuma suna neman hikima. 23Amma muna wa’azin Almasihu gicciyayye, dutsen tuntube ga yahudawa da kuma wauta ga Helinawa.

24Amma ga wadanda Allah ya kira, Yahudawa da Helinawa, muna wa’azin Almasihu a matsayin iko da kuma hikimar Allah. 25Gama wautar Allah tafi mutane hikima, kuma rashin karfin Allah yafi mutane karfi.

26Dubi kiranku, yan’uwa. Ba dukkan ku ke da hikima a ma’aunin mutane ba. Ba dukkan ku ke da iko ba. Ba dukkan ku ke da haifuwa ta sarauta ba. 27Amma Allah ya zabi abubuwan da suke wofi na duniya domin ya kunyatar da masu hikima. Allah ya zabi abin da ke marar karfi a duniya domin ya kunyatar da abinda ke mai karfi.

28Allah ya zabi abinda ke marar daraja da kuma renanne a duniya. Ya ma zabi abubuwan da ake dauka ba komai ba, domin ya wofinta abubuwan da ake dauka masu daraja. 29Ya yi wannan ne domin kada wani ya sami dalilin fahariya a gabansa.

30Domin abinda Allah ya yi, yanzu kuna cikin Almasihu Yesu, wanda ya zamar mana hikima daga Allah. Ya zama adalcinmu, da tsarkinmu da fansarmu. A sakamakon haka, kamar yadda nassi ya ce, “Bari mai yin fahariya, ya yi fahariya cikin Ubangiji.”

31

Copyright information for HauULB